logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi maraba da ziyarar da babban jami'in kare hakkin bil adama na MDD zai yi a wannan watan Mayu

2022-03-09 11:07:28 CRI

 

Wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva Chen Xu, ya shaidawa zama na 49 na hukumar kare hakkin bil-adama cewa, kasar Sin ta yi maraba da ziyarar da babbar kwamishiniyar hukumar kare hakkin bil-adama na MDD za ta kawo kasar Sin, ciki har da jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta a watan Mayu dake tafe.

Chen ya shaidawa kwamitin kare hakkin bil adama na MDD cewa, a yayin da duniya ke fuskantar kalubale daban-daban, wajibi ne kasashen duniya su hada karfi da karfe wajen tunkararsu, da daidaita bambance-bambancen da ke tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari, da kara amincewa da juna ta hanyar yin hadin gwiwa.

Chen ya kara da cewa, muna yaba wa babbar kwamishiniya da ofishinta, kan sanya yaki da rashin daidaito a matsayin abubuwa masu muhimmanci da ayyukan ofishin ya ba fifiko, da kara ba da gudummawa ga 'yancin tattalin arziki, da zamantakewa da al'adu da 'yancin samun ci gaba.

Ya kara da cewa, muna sa ran babbar jami'ar da ofishinta za su mutunta ‘yancin dukkan kasashe da kuma kare hakkin bil-adama da kuma hanyar ci gaban da kasashe suka zaba da kansu bisa yanayin kasashensu da inganta tattaunawa da hadin gwiwa, da kuma hada kai wajen tabbatar da ganin ana gudanar da aikin kare hakkin bil-adama a duniya cikin adalci, da ma'ana ta yadda zai kunshi kowa da kowa.

Ya kuma shaida wa majalisar cewa, ta hanyar mayar da jamaa a gaban komai, kasar Sin ta kuduri aniyar tabbatar da, kiyayewa da kuma ciyar da muhimman muradun daukacin al'ummar Sinawa gaba.(Ibrahim)