logo

HAUSA

Zhao Lijian: Amurka na yada karairayi game da matsayar Sin kan batun rikicin Ukraine

2022-03-09 20:10:48 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce Amurka na kitsa karairayi, a wani yunkuri na dorawa kasar Sin laifi, da haifar da fito na fito, don gane da matsayar kasar ta Sin kan batun Ukraine.

Zhao ya yi wannan tsokaci ne yayin taron manema labarai na yau Laraba, lokacin da yake martani kan rahotanni da wata kafar Amurka ta fitar mai cike da mumman manufa.

A baya bayan nan ne dai jaridar "New York Times" ta Amurka, ta buga wasu rahotanni 2, dake da goyon bayan hukumar tsaron Amurka, dake zargin Sin cewa wai tana da masaniyar shirin Rasha na kaiwa Ukraine hari.

A daya bangaren kuma, Zhao Lijian ya ce, Sin na adawa da takunkuman da ake kakabawa na kashin kai, wadanda ba su da goyon bayan dokokin kasa da kasa. Ya ce irin wadannan takunkumai ba abun da za su haifar, illa cutuwa ga dukkanin sassa, kana za su kara ta’azzara rarrabuwar kawuna da faito na fito.   (Saminu)