logo

HAUSA

MDD ta bayyana damuwa game da kisan ‘yan asalin Afrika da ‘yan sandan Amurka ke yi

2022-03-09 11:19:49 CRI



Babbar kwamishinar hukumar kare hakkin dan adama ta MDD Michelle Bachelet, ta ce mutane ‘yan asalin Afrika da dama, na mutuwa a hannun hukumomin tsaro a kasashe da dama, musammam ma a Amurka.

Michelle Bachelet ta bayyana cikin rahotonta na shekara yayin taro na 49 na hukumar kare hakkin dan adam cewa, a Amurka, kungiyoyin al’umma sun yi kiyasin ‘yan sanda sun kashe yan asalin Afrika da yawansu ya kai 266 a shekarar 2021.

A cewarta, wannan na nuna cewa, adadin ya ninka har sau uku na yiwuwar mutuwar fararen fata a hannun ‘yan sanda. Tana mai cewa, wasu bincike sun nuna cewa adadin na iya zarce wannan.

A baya-bayan nan, hukumar kare hakkin dan adam ta MDD ta karbi rahoton da ya bayyana cewa, ana kara samun wariyar launin fata a tsarin shari’ar laifuffuka na Amurka.

Misali, George Floyd, BaAmurke bakar fata da ya mutu a Minneapolis, sanadiyyar danne masa wuya na tsawon mintuna 8 da dan sandan Amurka ya yi a watan Mayun 2020, lamarin da ya haifar da zanga-zangar kin wariyar launin fata da cin zalin da ‘yan sanda ke yi a Amurka da ma duniya baki daya. (Fa’iza Mustapha)