logo

HAUSA

MDD ta yi murnar ranar mata ta duniya tana mai jinjinawa shugabancin matan

2022-03-09 10:24:06 CRI

 

MDD ta yi murnar ranar mata ta duniya a jiya Talata, inda ta jinjinawa shugabancin mata a dukkan fannonin rayuwa tare da kira da a tabbatar da daidaiton jinsi.

Manyan jamian MDD da masu rajin kare hakkokin mata da yan siyasa da sauran mutane daga fadin duniya ne suka yi murnar ranar ta 8 ga watan Maris ta kafar intanet.

Da yake yabawa shugabancin mata, Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi gargadin cewa ana samun koma baya game da yanayin kare hakkokin mata a bangarori da dama, yana mai bayar da misali da tasirin annobar COVID-19.

Ya ce a dalilin wannan annoba, yan mata ba sa zuwa makaranta, mata kuma ba su da damar zuwa aiki, lamarin dake bayar da gudunmuwa ga karuwar talauci da rikice-rikice.

A cewarsa, ba za a iya cin galaba a kan annobar ba yayin da hannun agogo ke komawa baya game da daidaiton jinsi. Yana mai cewa, akwai bukatar mayar da hannun agogon bisa alkiblar da ta dace. 

A nata bangaren, babbar daraktar hukumar kula da harkokin mata ta MDD Sima Bahous, cewa ta yi, batutuwa masu sarkakiya na kawo cikas ga kokarin samun daidaiton jinsi a duniya.

Ta ce saboda sauyin yanayi da lalacewar muhalli, rashin tsaro na karuwa a tsakanin daidaikun mutane da ma kasashe, inda lamarin ke mummunan tasiri kan mata da yan mata.

Ta kara da cewa, duniya na iya ba mata fifiko yayin da ake aiwatar da tsare-tsare da daukar matakai, tare da kokarin tabbatar da daidaiton jinsi cikin dabaru da dokokin kasa da kasa. (Faiza Mustapha)