logo

HAUSA

‘Yar sama jannati ta kasar Sin ta aiko da sakon taya muranar ranar mata daga sararin samaniya

2022-03-08 17:01:19 CRI

'Yar sama jannati ta biyu a kasar Sin Wang Yaping, wadda yanzu haka ke aiki na tsawon watanni 6 a tashar sararin samniya ta kasar Sin, ta aike da sakon taya murna ga ofishin MDD dake Geneva na Switzerland, inda take taya mata a ko ina, murnar zagayowar ranar mata ta duniya dake gudana a yau Talata, 8 ga watan Maris.

Cikin sakon, Wang Yaping ta ce tana fatan ‘yan matan dake da burin zama ‘yan sama jannati za su yi kokarin cimma burin ganin matattarar taurari. Ta ce “wata rana kafin ku ankara, za ku ga cikar burinku”. (Fa’iza Mustapha)