logo

HAUSA

Yakin da kasar Sin ta yi kan laifukan da suka shafi muhalli yana tasiri

2022-03-08 15:14:28 CRI

Wani rahoton aiki da hukumar koli mai gabatar da kararraki ta kasar Sin ta gabatar, ya nuna cewa, an samu sakamako mai gamsarwa game da yaki da laifuffukan da suka shafi muhalli.

A cewar rahoton wanda aka gabatar Talatar nan ga zama na biyar, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, domin yin nazari a kai, ya bayyana cewa, a bara kasar Sin ta gurfanar da mutane 49,000 bisa laifukan da suka sabawa doka da suka shafi muhalli, wanda shi ne raguwar farko da aka samu a cikin shekaru takwas.