logo

HAUSA

Zhao Lijian: Ya kamata a binciki ayyukan sojin Amurka masu nasaba da gwaje gwajen kwayoyin halittu

2022-03-08 19:02:53 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce kamata ya yi a binciki ayyukan sojin Amurka, masu nasaba da makamai masu guba a gida da waje, domin sassan kasa da kasa su tantance abubuwan da Amurkan ke aiwatarwa.

Zhao na wannan tsokaci ne yayin taron manema labarai na yau Talata, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa, game da cibiyar gwaje gwajen kwayoyin halittu ta Amurka dake kasar Ukraine.

Zhao Lijian, ya ce cibiyar gwaje gwajen mai nasaba da ayyukan soji ta Amurka dake Ukraine, dan karamin bangare ne kawai na makamantan ta da Amurka ke gudanarwa.

Amurka na da manufar da ta kira “Ta karfafa tsarin kiwon lafiya na duniya”, wanda a karkashin ta, ma’aikatar tsaron kasar ke daukar nauyin dakunan gwaje gwaje na kwayoyin halittu har 336 a kasashe 30.   (Saminu)