logo

HAUSA

Rasha da Ukraine sun kawo karshen shawarwarin zaman lafiya karo na 3 ba tare da wani gagarumin sakamako ba

2022-03-08 09:36:16 CRI

Masu shiga tsakani na kasashen Rasha da Ukraine, sun gaza cimma wani gagarumin sakamako a zagaye na uku na tattaunawar zaman lafiya da suka yi a kasar Belarus jiya Litinin.

Mai taimakawa shugaban kasar Rasha kana jagowan tawagar Rasha a tattaunawar Vladimir Medinsky, ya bayyana cewa, tattaunawar za ta ci gaba a kan batutuwan siyasa da na soja. Duk da haka, ya yi wuri a yi magana game da wani ci gaba da aka samu.

Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, masu shiga tsakani na Rasha, sun zo da wasu takardu masu tarin yawa, ciki har da takamaiman yarjejeniyoyi, amma bangaren Ukraine bai iya sanya hannu a kansu nan take ba, inda ya kwashe dukkan takardu zuwa gida domin yin nazari a kansu.

Bangarorin biyu sun yi magana kan batun kwashe fararen hula, kuma bangaren Ukraine ya tabbatar wa Rasha cewa, hanyoyin kai kayayyakin jin kai za su fara aiki a yau Talata.

Mykhailo Podoliak, mai ba da shawara ga shugaban ofishin shugaban kasar Ukraine, ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan tattaunawar cewa, akwai kyakkyawan ci gaba, idan ana batun inganta dabaru na hanyoyin jin kai. (Ibrahim)