logo

HAUSA

Xi Jinping ya zanta da shugabannin Faransa da Jamus

2022-03-08 19:32:39 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta kafar bidiyo da shugaba Emmanuel Macron na faransa, da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da yammacin Talatar nan, inda suka maida hankali ga tattauna yanayin da ake ciki a kasar Ukraine.

Yayin zantawar ta su, shugaba Macron da Mr. Scholz, sun godewa gudummawar kasar Sin, don gane da tallafawa manufar samar da agajin jin kai, sun kuma bayyana aniyar su ta karfafa sadarwa, da tsare tsare tare da bangaren Sin, domin ingiza wanzar da zaman lafiya, da goyon bayan tattaunawa.

A nasa bangaren, Xi Jinping ya jaddada cewa, abu mafi muhimmanci shi ne dakile kara kazantar al’amura. Ya ce Sin na goyon bayan kasashen Faransa da Jamus, a fannin kafa tsarin daidaito, mai dacewa, kuma wanda zai wanzar da tsaron Turai bisa moriyar nahiyar.  (Saminu)