logo

HAUSA

Majalisar Dokokin Kasar Sin Ta Fara Cikakken Zama Na Biyu Na Taronta na 5

2022-03-08 11:03:52 CRI

Taro na 5 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) karo na 13, wato majalisar dokokin kasar, ya fara cikakken zamansa na biyu a yau Talata.

Xi Jinping da sauran shugabannin kasar Sin sun halarci taron a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing.

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar NPC, Li Zhanshu, ya gabatar da rahoton ayyukan kwamitin ga taron.

Mambobin majalisar sun kuma saurari rahoton ayyukan kotun koli da shugaban kotun Zhou Qiang ya gabatar, tare da sauraron rahoton hukumar koli mai kula da kararrakin jama’a daga shugaban hukumar, Zhang Jun. (Fa’iza Mustapha)