logo

HAUSA

Kasar Sin Na Daya Daga Cikin Kasashe Mafiya Tsaro A Duniya

2022-03-08 11:12:38 CRI

Wani rahoton aiki da kotun kolin jama'a ta kasar Sin (SPC) ta fitar Talatar nan, na nuna cewa, kasar Sin na daya daga cikin kasashen da suka fi zaman lafiya a duniya.

Rahoton wanda aka mika wa majalisar wakilan jama’ar kasar Sin domin tattaunwa, ya bayyana cewa, adadin manyan laifuffuka iri-iri guda takwas, kamar kisan kai, da fyade da kuma satar mutane, ya ragu matuka, yayin yawan irin wadannan laifuffuka da ke cikin laifuffuka duka shi ma ya ragu sosai

A cewar rahoton kotun kolin, kasar Sin ta sanya hukunci mai tsauri kan laifuffukan da suka shafi cin hanci da rashawa kamar yadda dokokin kasar suka tanada, A hannun guda kuma a shekarar 2021, kotunan kasar Sin, sun kammala yanke hukunci kan kararraki 23,000 da suka shafi cin hanci da rashawa, wadanda suka shafi mutane 27,000. (Ibrahim)