logo

HAUSA

Xi ya jaddada bukatar aiwatar da ayyukan soji bisa dokokin kasa

2022-03-07 20:54:43 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar aiwatar da ayyukan sojin kasa bisa doka, da kara kyautata bin ka’idojin aikin tsaron kasa, da gina tsarin aikin soji mai nagarta.

Xi ya yi wannan tsokaci ne, yayin taron wakilan rundunar ‘yantar da al’umma, da rundunar ‘yan sandan kasa, a bangaren taro na 5 na majalissar wakilan jama’ar kasar Sin ta 13, wanda ke gudana yanzu haka.  (Saminu)