logo

HAUSA

Wang Yi: Sin na martaba hadin gwiwar ta da kasashen Afirka

2022-03-07 19:43:22 CRI

Babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce Sin na martaba hadin gwiwar ta da kasashen Afirka, kuma ba ta taba saba alkawarin ta ba.

Wang Yi, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Litinin din nan, ya ce cikin shekarun baya bayan nan, Sin ta gina layukan dogo da suka kai tsayin sama da kilomita 10000, da manyan hanyoyin mota masu tsayin kimanin kilomita 100000, da tashoshin ruwa kimanin 100, da kuma tarin asibitoci da makarantu a nahiyar Afirka.

Wang ya kara da cewa, ba wani batu na tarkon bashi, sai dai kawai tsabar ayyukan hadin gwiwa tsakanin sassan biyu.

Ya ce Sin za ta cika alkawarin ta, na samarwa Afirka alluran rigakafin cutar COVID-19 har biliyan 1, za ta kuma taimakawa nahiyar wajen samar da karin rigakafin a cikin gida, tare da tallafawa nahiyar wajen cimma nasarar yiwa al’ummun ta da za su kai kaso 60 bisa dari rigakafin cutar a wannan shekara ta bana. (Saminu)