logo

HAUSA

Saudiyya ta soke haramcin zirga-zirga tsakaninta da wasu kasashe 17, ciki har da Nijeriya

2022-03-07 14:46:42 CRI

A jiya, kasar Saudiyya ta sanar da soke haramcin tafiye-tafiye a tsakaninta da wasu kasashe 17, ciki har da Nijeriya. Sauran kasashen sun hada da Afirka ta kudu da Namibia da Botswana da Zimbabwe da Lesotho da Swaziland da Mozambique da Malawi da Mauritius da Zambia da Madagarscar da Angola da Seychelles da Comoros da Habasha da kuma Afghanistan.

Ban da haka, gwamnatin Saudiyya ta kuma soke muhimman matakan kandagarkin cutar Covid-19, sai dai wajibi ne a sanya marufin baki da hanci a masallatan Makka da na Madina da sauran wuraren ibada. Karkashin sabuwar manufar, babu bukatar yi wa maziyarta da suka isa Saudiyya gwajin cutar ko kuma nuna sakamakon gwajin da aka yi musu, amma wajibi ne su sayi inshora don biyan kudin jinya idan sun harbu da anobar COVID-19. (Lubabatu)