logo

HAUSA

Kasar Sin tana nazarin ba da karin kujeru ga mata da jama'a dake yankunan karkara a majalisar dokokin kasar

2022-03-07 10:56:18 CRI

’Yan majalisar dokokin kasar Sin suna nazarin wani daftarin kuduri, da zai duba yiwuwar baiwa mata da mutane daga yankunan karkara karin kujeru a majalisar dokokin kasar 

A ranar Asabar din da ta gabata ce, aka mika daftarin yanke shawara, kan kason kuri’u da kuma zaben wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 14 ga zaman taro na biyar na majalisar wakilan jama'ar kasar karo na 13, domin tattaunawa.

A cewar daftarin, ya kamata adadin ’yan majalisa daga yankunan karkara a majalisar wakilai ta 14, musamman ma’aikatan sa-ido, da manoma da kwararru ya zarce na majalisar wakilan kasar ta 13. 

Daftarin ya kara da cewa, majalisar NPC ta 14, za ta samu karin wakilai daga bangaren ma'aikata ’yan ci-rani fiye da na majalisar wakilai ta 13, inda aka bayyana cewa, bisa ka'ida, yawan wakilai mata a majalisar NPC ta 14, zai zarce na majalisar wakilai ta 13.

Bisa da daftarin, adadin 'yan majalisa daga kananan kabilu, zai kai kusan kashi 12 cikin dari na jimillar wakilai.

Daftarin ya zayyana cewa, za a kammala zaben wakilan ne a watan Janairun 2023.  (Ibrahim Yaya)