logo

HAUSA

Yadda Gasar Olympic ta Beijing ta hada kan al’umma zai haskaka makomar ’yan Adam

2022-03-07 17:06:22 CRI

A gun taron manema labarai da aka kira a yau Litinin a gefen manyan taruka biyu da ke tafe a nan birnin Beiijng, dan majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya bayyana godiya ga dukkan wadanda suka halarta ko nuna goyon baya ga gasar Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing.

Wang Yi ya ce, a kokarin da kasar Sin da ma gamayyar kasa da kasa suka yi, gasar Olympic ta samu cikakkiyar nasara, kuma kimanin kasashe 70 da kungiyoyin kasa da kasa 170 sun halarci bikin bude gasar, wadanda suka nuna goyon bayansu ga kasar Sin.

Ya kara da cewa, nasarar gasar ba ma kawai nasara ce ga kasar Sin ba, har ma nasara ce ga duniya baki daya, kuma ba nasara ce kawai ga wasanni ba, har ma ta kasance nasarar hada kan al’ummar duniya. (Lubabatu)