logo

HAUSA

Wang Yi: Har kullum burin Sin shi ne wanzar da daidaito

2022-03-07 20:12:03 CRI

Babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce a wannan duniya mai bukatar daidaito da sauye sauye, har kullum Sin na yayata bukatar wanzar da daidaito da cimma nasarori, tana kuma goyon bayan dukkanin kyawawan manufofin da tarihi ke maraba da su.

Wang ya kara da cewa, matakan aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya na ci gaba da kankama, duk kuwa da kalubale da ake fuskanta, ciki har da batun yaki da annobar COVID-19.

Ya ce Sin na kan hanyar zama kasuwa mai tasiri, kuma jigon sauyawar kasashe masu tasowa, daga mabiya zuwa masu wucewa gaba, har su kai ga zama masu nuna misali a tsarin jagorancin duniya. Kaza lika Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran kasashe, wajen aiwatar da muradun samar da ci gaba na duniya ko GDI a takaice.   (Saminu)