logo

HAUSA

Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda hudu kan warware rikicin Ukraine

2022-03-07 16:30:29 CRI

   

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana matsayin kasar Sin da shawarar da ta dauka kan warware rikicin kasar Ukraine a halin yanzu, yayin taron manema labarai na taruka biyu da ake gudanarwa Litinin din nan.

Wang Yi ya ce, kasar Sin ta yi imanin cewa, idan har ana son warware rikicin da ake fama da shi a halin yanzu, wajibi ne mu mutunta manufofi da ka'idojin kundin tsarin mulkin MDD, da mutunta juna da kare 'yancin kai da yankunan dukkan kasashen duniya, haka kuma dole ne mu martaba ka'idar rashin raba kan harkokin tsaro, da daidaita matsalolin tsaro na bangarori, wajibi ne a martaba sasanta rikice-rikice ta hanyar tattaunawa da sasantawa cikin lumana, dole ne mu mai da hankali kan dorewar zaman lafiyar yanki da samar da daidaito, inganci da dorewar tsarin tsaro a Turai.

Wang Yi ya kara da cewa, kasar Sin ta yi imanin cewa, yayin da ake kara tsananta halin da ake ciki, za a kara ci gaba da yin tattaunawar zaman lafiya, yayin da ake kara samun sabanin ra'ayi, ya zama wajibi a zauna a yi shawarwari. Kasar Sin tana son ci gaba da taka rawa mai ma'ana, wajen shawo kan zaman lafiya, da sa kaimi ga yin shawarwari, kuma tana son yin hadin gwiwa da ragowar kasashen duniya, wajen shiga tsakani a lokacin da ake bukata. (Ibrahim)