logo

HAUSA

MDD ta yi Allah wadai da hari kan masallaci a Pakistan

2022-03-07 11:43:40 CRI

Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da harin ta’addanci da aka kaddamar kan masallaci a yankin Peshawar na kasar Pakistan inda aka kashe gomman mutane.

A sanarwar da aka baiwa manema labaru, kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da babbar murya game da mummunan harin na matsorata ’yan ta’adda, wadanda suka kaddamar kan masallacin Koocha Risaldar dake yankin Peshawar, a kasar Pakistan, a ranar Juma’a 4 ga watan Maris na shekarar 2022.

MDDr ta bukaci a binciko wadanda ke da hannu wajen shirya harin, da masu daukar nauyinsa, da kuma masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci domin gurfanar da su a gaban shari’a, kana an bukaci dukkan jihohin kasar da su hada kai da gwamnatin Pakistan.

Sanarwar ta bayyana cewa, ayyukan ta’addanci mummunan laifi ne wanda ba za a taba laminta ba, kuma ba tare da la’akari da manufar maharan ba, sannan an bukaci dukkan kasashen duniya da su hada kai wajen kawar da duk wata barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa wanda ayyukan ta’addanci ke haifarwa.

Harin kunar bakin waken da aka kaddamar a daidai lokacin da ake sallar Juma’a, ya yi sanadiyyar kashe mutane 63, sannan wasu kusan 200 sun samu raunuka. (Ahmad)