logo

HAUSA

Ghana ta shirya kasaitaccen bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai

2022-03-07 11:18:24 CRI

A ranar Lahadi kasar Ghana ta gudanar da kasaitaccen bikin murnar cika shekaru 65 da samun ’yancin kan kasa daga Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya, inda aka gudanar da fareti na kasa a yankin Cape Coast, babban birnin Shiyyar Tsakiyar kasar.

Da yake gabatar da jawabi a wajen faretin, shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na cigaba da aikin tabbatar da tsaron yankunan kasar, da zaman lafiya, da tsaron kasar Ghana a yayin da ake fama da matsalolin tashe-tashen hankula a wasu bangarori na shiyyar yammacin Afrika.

Akufo-Addo ya ce, kokarin da suke na tabbatar da sauye-sauyen tattalin arzikin Ghana, da kafa tubalin ci gaban kasa, da samar da makoma mai kyau ga kasar, ba zai taba cimma nasara ba matukar aka gaza tabbatar da tsaron kan iyakokin kasar, ta yadda za a baiwa al’ummar kasar Ghana damar samun ’yancin walwala don su gudanar da al’amurransu na yau da kullum cikin yanayin zaman lafiya da tsaro.

Shugaban ya bayyana damuwa game da karuwar hare-haren ta’addanci daga yankin Sahel har zuwa jihohin yankunan kudancin gabar teku, inda ya bukaci ’yan kasar Ghana da su baiwa jami’an tsaro hadin kai yayin da suke gudanar da ayyukansu na tabbatar da tsaron kasa daga barazanar hare-hare daga ketare da kuma rikice-rikice na cikin gida. (Ahmad)