logo

HAUSA

Masu fafutuka na Afirka sun bukaci saka jari dake shafar jama'a don gaggauta komawa ga kare muhalli

2022-03-07 10:47:54 CRI

Masu fafutukar kare muhalli a nahiyar Afirka sun bayyana cewa, kokarin samar da tsari na adalci, da zai kunshi kowa tare da sauyawa ga tsarin kare muhalli a Afirka, zai tabbata ne kawai, idan gwamnatoci da masu ba da lamuni, suka karkata galibin albarkatunsu wajen aiwatar da wasu matakai daga tushe da nufin dakile matsalar sauyin yanayi.

Masu fafutukar sun bayyana a cikin wata sanarwa da suka fitar a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa, dorewar rage fitar da sinadarin Carbon a nahiyar Afirka, yana bukatar sanya al'ummomi a kan turbar dakile sauyin yanayi, da samar da kudaden da za su daidaita matsalar.

Tracy Sonny, 'yar kasar Botswana kuma mamba a gamayyar kungiyoyin yaki da sauyin yanayi na Afirka (PACJA) mai hedkwata a Nairobin Kenya, ta jaddada cewa, akwai bukatar hanzarta fito da manufofin da suka shafi jama'a, da dokoki da kuma tsarin samar da kudade, don gaggauta komawa ga tsarin kiyaye muhalli a nahiyar dake da tsananin zafi.

Jiata Ekelle, wata kwararre kan yanayi da dorewa daga Najeriya, ta ba da shawarar cewa, ya kamata yankin kudu da hamadar Sahara, ya zuba jari a shirye-shiryen farfado da al'umma da suka hada da farfado da dazuzzuka, da farfado da filayen da suka lalace da makamashi mai tsafta a yayin da yankin ke kan hanyar bunkasa hanyoyin kare muhalli. (Ibrahim)