logo

HAUSA

“Taruka biyu” sun isar da kyakkyawan sako ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya

2022-03-07 14:38:05 CRI

A ranar 5 ga wata ne, aka bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) a nan birnin Beijing, kuma bakin da aka ba su goron gayyatar halartar taron, sun nuna yabo da aminci ga nasarorin da kasar Sin ta samu cikin ’yan shekarun da suka gabata da ma yadda kasar ta kiyaye ci gaban tattalin arzikinta duk da yakin da take yi da annobar Covid-19, har wa yau sun bayyana cewa, sakon da “taruka biyu” (NPC da CPPCC) suka isar, ya karfafa gwiwar kasashen duniya game da bunkasuwar kasar Sin.

A shekarar 2021, kasar Sin ta yi kokarin tabbatar da ganin bunkasuwarta ba tare da gurbata muhalli ba, tare da dada samar da dabarunta na daidaita matsalolin muhalli a fadin duniya, kuma an sake rubuta burin da kasar Sin ta sanya gaba na rage fitar da hayakin Carbon a cikin rahoton aikin gwamnati da aka gabatar a taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin na wannan shekara. A game da wannan, Siddharth Chatterjee, babban jami’in MDD da ke kasar Sin ya bayyana cewa,“A kokarin da ake na tinkarar sauyin yanayin duniya, kasar Sin ta yi alkawarin cewa, yawan hayaki mai dumama yanayin duniyarmu da za ta fitar zai kai matsayin koli kafin shekarar 2030, sannan za ta yi kokarin samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin kafin shekarar 2060, alkawarin da ya samu yabo matuka daga babban sakataren MDD Antonio Guterres, wanda ya gode wa kasar Sin kan gudummawar da ta baiwa bangaren shawo kan matsalar sauyin yanayin duniya, kuma hakan zai taimakawa duniya wajen gaggauta tinkarar matsalar.” (Lubabatu)