logo

HAUSA

Amurka ta tattauna batun sanya takunkumin man fetur kan Rasha

2022-03-07 12:00:01 CRI

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya bayyana a wani shirin kafar yada labarai ta CNN a ranar 6 ga watan Maris cewa, shugaban kasar Amurka Joe Biden, da sauran sassan ma’aikatun gwamnatin kasar suna tattaunawa game da sanyawa Rasha takunkumi a fannin albarkatun mai. Amurka za ta hada kai da kawayenta na kasashen Turai, domin tabbatar da cewa matakan da za a dauka ba za su shafi tsarin samar da albarkatun mai a kasuwannin duniya ba. Blinken ya kuma bayyana cewa, Amurka za ta taimakawa kasar Poland don samar da jiragen yaki ga kasar Ukraine, kana za ta taimakawa Poland ta cike gibin tsaronta bayan taimakon da ta baiwa Ukraine.

A wannan rana ta 6 ga watan Maris, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana a tattaunawarsa ta wayar tarho da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron cewa, sojojin Rasha da jami’an kasar Ukraine za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na tsaron tashar nukiliya ta Zaporizhzhia dake kudancin kasar Ukraine. Sannan matakin tiririn zafi na tashar makamashin nukiliyar Zaporizhzhia yana cikin kyakkyawan yanayi, kamar yadda hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta sanar. Fadar Elysee ta shugaban kasar Faransa ta fidda takardar bayani a wannan rana cewa, shugaba Macron ya bukaci Putin ya tabbatar da tsaron lafiyar fararen hula a cibiyoyin nukiliyar Ukraine. Sannan ya bukaci a mutunta dokokin kula da ayyukan jinkan na kasa da kasa, da tabbatar da baiwa fararen hula kariya da kuma ba da damar shigar da kayayyakin tallafi. (Ahmad)