logo

HAUSA

Kafofin watsa labaran kasa da kasa: Taruka biyu na Sin na da babbar ma’ana ga zamantakewar al’ummun duniya

2022-03-06 16:04:33 CRI

Kamfanin watsa labarai na kasar Kenya wato KBC, ya gabatar da wani sharhi dake cewa, taruka biyu na kasar Sin wadanda ke gudana a birnin Beijing na kasar suna jawo hankalin al’ummun kasashen duniya matuka, musamman ma batun dake shafar shawarar ziri daya da hanya daya, saboda shawarar tana amfanar dukka duniya, har ma tana taka muhimmiyar rawa wajen cudanyar tattalin arzikin duniya. Sharhin ya kara cewa, kasar Sin abokiyar cinikayya mafi girma ta kasashen Afirka ce, wadda ke zuba jari mafi yawa a nahiyar, musamman ma a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasashen Afirka suna cin gajiya daga jarin da kasar Sin ke zubawa a nahiyar, misali a bangarorin manyan ayyukan gina kayayyakin more rayuwar jama’a da kuma kiwon lafiya. Don haka batutuwan da za a tattauna yayin taruka biyu na kasar Sin suna da babbar ma’ana ga kasashen Afirka, ban da haka, shugabannin kasashen Afirka da dama suna sa ran za su kara kyautata huldar dake tsakanin kasashensu da kasar Sin, tare kuma da kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu.

Jaridar “Observer” ta kasar Pakistan ta wallafa wani sharhi a ranar 4 ga wata, inda aka bayyana cewa, kasar Sin ta samu amincewa daga masu zuba jari a fadin duniya, bisa salon karuwar tattalin arzikinta na ci gaba mai dorewa, yanzu haka ana gudanar da taruka biyu a kasar Sin, inda ake tabbatar da cewa, idan kasar Sin ta ci gaba da samun wadata, tabbas ne daukacin kasashen duniya za su ci gajiya daga ci gaban kasar ta Sin. (Jamila)