logo

HAUSA

Xi Jinping ya gabatar da amsar wasika ga shugaban IOC Tomas Bach

2022-03-06 20:03:23 CRI

A ranar 2 ga watan Maris, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da amsar wasika ga shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasa da kasa IOC, Tomas Bach.

Xi Jinping, ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing ta 2022 ta kammala cikin nasara. Kasar Sin ta samu cikakkiyar nasarar karbar bakuncin gasar, kuma ingantaccen tsarin da kasar ta bi wajen karbar bakuncin gasar, ya baiwa duniya damar jin dadi da farin cikin gasar ta Olympic, wadda ta samu yabo daga al’ummun kasa da kasa. Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, wannan babbar nasara ce ga al’ummar duniya.(Ahmad)