logo

HAUSA

Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Tattauna Ta Wayar Tarho Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Game Da Huldar Kasashen Biyu Da Kuma Batun Ukraine

2022-03-06 16:02:22 CRI

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, a ranar Asabar ya tattauna ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, game da huldar dake tsakanin Sin da Amurka da kuma batutuwan dake shafar Ukraine bisa gayyatar da Blinken ya yi masa.

Wang ya ce a halin yanzu, babban abinda huldar dake tsakanin Sin da Amurka zata fi mayar da hankali shine, batun daga matsayi da kuma aiwatar da yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma matsaya kansu a taron da suka gudanar ta kafar bidiyo, ya kara da cewa, kasar Sin ta bayyana matukar damuwa game da kalamai na baya bayan nan da Amurka ta furta da kuma abubuwan da ta aikata wadanda sun ci karo da manufofin da ake son cimmawa karkashin yarjejeniyoyin kasashen biyu.

Blinken ya bayyanawa bangaren kasar Sin ra’ayoyin Amurka, da matsayarta, game da halin da ake ciki a Ukraine. Wang yace, abubuwan dake faruwa kan batun Ukraine, wasu batutuwa ne da kasar Sin bata son ganin faruwar hakan.

Batun Ukraine al’amari ne mai sarkakiya, wanda ba kawai ya shafi hakikanin manufofin kasa da kasa bane, har ma ya shafi bukatun tsaron bangarori daban-daban, a cewar Wang, inda ya bukaci a mayar da hankali, ba kawai kan batun warware rikicin dake faruwa a halin yanzu ba, har ma da tabbatar da samun dorewar zaman lafiyar shiyyar baki daya.(Ahmad)