logo

HAUSA

​Xi: Ya dace baiwa fannin inganta dabarun ayyukan noma matukar muhimmanci

2022-03-06 21:19:26 CRI

Da yammacin yau Lahadi, 6 ga watan Maris, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci wakilan fannonin ayyukan gona, da kyautata jin dadin al’umma da walwalar jama’a dake halartar taro na biyar na majalisar ba da shawara kan al’amurran siyasar kasar Sin ta 13, tare da halartar taron hadin gwiwa na jin ra’ayoyi da shawarwari.

Ya jaddada cewa, yayin aiwatar da shirin bunkasa yankunan karkara, aiki na farko shi ne, tilas ne a tabbatar da samar da muhimman kayayyakin amfanin gona, musamman abinci, domin a tabbatar da jin dadin zaman rayuwar al’umma.(Ahmad)