logo

HAUSA

Filayen gasar Olympics na lokacin sanyi za su ingiza ci gaban wasannin kankara na Sin

2022-03-06 16:39:32 CRI

A ranar 4 ga wata, an kaddamar da gasar Olympics ta lokacin sanyi da kuma taro karo na 5 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 13 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar, wasu mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar wadanda ke halartar taron sun bayyana cewa, Beijing ne birni na farko a fadin duniya, wanda ya shirya gasar Olympics na lokacin zafi da na lokacin sanyi, don haka an gina wasu filayen wasa da dakunan wasa da dama a birnin, duk wadannan za su taka rawa kan dauwamammen ci gaban duniya.

A bayyane an lura cewa, birnin Beijing ya samu manyan sauye-sauye tsakanin shekarar 2008 zuwa 2022, haka kuma an samu saurin ci gaban kasar Sin cikin wadannan shekarun da suka gabata, to game da yadda ake amfani da filayen wasannin Olympics bayan da aka kammala gasar? Mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar kuma mataimakin shugaban sashen tsara gine-gine na kwamitin shirya gasar Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing Shen Jin ya yi tsokaci cewa, gina filayen wasa bisa ma’aunin gasar Olympics, tare kuma da yin la’akari kan yadda za a sake yin amfani da su bayan kammala gasar, aiki ne mafi muhimmanci da sashen tsara gine-gine na kwamitin shirya gasar Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing ya yi, inda ya bayyana cewa, yayin da ake fasalin filayen wasa, an fi mai da hankali kan batun yadda za a gyara ko kuma sake yin amfani da su a nan gaba. (Jamila)