logo

HAUSA

Babban jami’in MDD ya bayyana damuwa game da rikicin siyasar Libya

2022-03-06 16:07:42 CRI

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya tattauna ta wayar tarho a ranar Juma’a da Abdul-Hamid Dbeibah, firaministan gwamnatin hadin kan kasar Libya, inda suka tattauna game da cigaban da aka samu na baya bayan a kasar.

A sanarwar da ofishinsa ya baiwa manema labarai, Guterres, ya bayyana matukar damuwa game da halin da ake ciki na fuskantar barakar siyasa a kasar Libya, wanda hakan babbar barazana ce ga samun dorewar zaman lafiyar Libya.

Babban sakataren ya jaddada bukatar dukkan bangarori masu ruwa da tsaki a kasar dasu kai zuciya nesa, kana ya nanata aniyar MDD na yin Allah-wadai wajen amfani da dukkan hanyoyin tashin hankali, da cin zarafi, da kuma kalaman kiyayya.

Majalisar wakilan kasar Libya, wato majalisan dokokin kasar, a ranar Talata, ta jefa kuri’ar amincewa da kafa sabuwar gwamnati wacce zata maye gurbin gwamnatin da Dbeibah ke jagoranta. An kuma rantsar da sabuwar gwamnatin a ranar Alhamis.

A watan Satumbar shekarar 2021, ‘yan majalisar wakilan kasar sun kada kuri’ar kin goyon bayan gwamnatin Dbeibah, inda suka mayar da gwamnatin ta rikon kwarya. A ranar 10 ga watan Fabrairu, ‘yan majalisar suka amince da gagarumin rinjaye inda suka zabi Fathi Bashagha a matsayin sabon firaministan kasar.(Ahmad)