logo

HAUSA

An Bude Taron Majalisar NPC Na Bana

2022-03-05 10:21:05 CRI


Da safiyar yau Asabar ne aka bude taron shekara-shekara, na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ko NPC a takaice, a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran jagororin kasar sun halarci bikin bude taron na 5, na majalissar ta 13, a babban dakin taruwar jama’a.

Yayin bude taron, firaministan Sin Li Keqiang, ya gabatar da rahoton ayyukan gwamnati, a madadin majalisar gudanarwar kasar. Cikin rahoton, an sanya burin daga yawan GDPn kasar da kaso 5.5 bisa dari a shekarar 2022. Kaza lika a shekarar nan ta 2022, Sin na fatan samar da karin sabbin guraben ayyukan yi sama da miliyan 11 a birane, tare da rage adadin marasa ayyukan yi a biranen zuwa kasa da kaso 5.5.

Har ila yau, rahoton ya ce, manufar raya tattalin arzikin Sin ba ta sauya ba, inda ake fatan wanzar da ci gaba na tsawon lokaci. Yayin da kasar za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau na dorewar ci gaba, ciki har da damammakin kirkirar sana’o’i, da ingiza kirkire-kirkire, kuma tuni kasar ta samu gogewa a fannonin tunkarar kalubale da hadurra.

Rahoton ya kara da cewa, ko shakka babu, tattalin arzikin kasar Sin zai jure duk wani matsi, zai kuma ci gaba da bunkasa sannu a hankali tsawon lokaci a tarihi.    (Saminu)