logo

HAUSA

Sojoji 27 da wasu ‘yan ta’adda 70 sun mutu yayin wani hari a yankin tsakiyar Mali

2022-03-05 11:34:36 CRI

 

Gwamnatin kasar Mali ta sanar da cewa, sojojinta 27 da ‘yan ta’adda 70 sun mutu yayin wani hari da aka kai wa sansanin sojojin kasar dake Mondoro na yankin tsakiyar kasar.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar jiya Juma’a, ta ruwiato cewa, an kai wani hari mai muni a sansanin ta hanyar amfani da motocin dake dauke da bama-bamai da safiyar jiya Juma’a. Lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojojin kasar 27, da jikkatar wasu 33, sai wasu 7 da suka bata, baya ga kayayyakin da aka lalata a sansanin.

A cewar sanarwar, dakarun musammam da aka tura yankin cikin gaggawa, sun kashe ‘yan ta’adda 47 da safiyar jiyan, sai kuma wasu 23 da suka kashe da rana.

Tun daga shekarar 2012, Mali ke fama da matsaloli masu tsanani ta fuskar tsaro da siyasa da tattalin arziki. Ayyukan ‘yan aware da na masu rajin jihadi da rikicin kabilanci, sun yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba wasu dubbai da mastugunansu a kasar ta yammacin Africa. (Fa’iza Mustapha)