logo

HAUSA

Sin ta yi kokarin yaki da laifuffukan sacewa da sayar da mata da yara

2022-03-05 11:29:55 CRI

A cikin rahoton aikin gwamnatin kasar Sin da aka gabatar a yau Asabar, an ce, dole ne a ci gaba da kokarin yaki da laifuffukan sacewa, da sayar da mata da yara, don tabbatar da hakkin mata da yara.

Kana an yi bayanin cewa, ya kamata a sa kaimi ga kyautata zaman rayuwar jama’a, da tabbatar da zaman lafiyar al’ummar kasa. Ya kamata a yi kokarin kyautata tsarin tafiyar da harkokin zamantakewar al’ummar kasa, da inganta karfin kananan jami’an gwamnati. Za a ci gaba da gudanar da ayyukan raya zamantakewar al’umma, da nuna goyon baya ga kungiyoyin zamantakewar al’umma, da aikin jin kai, da samar da hidimar sa kai da sauransu.

Kana a cikin rahoton, an jaddada cewa, ya kamata gwamnatoci a matakai daban daban, da ma’aikatansu, su mai da hankali ga hidimtawa jama’a, da nazarin yanayin zaman rayuwar jama’a, da gudanar da ayyuka yadda ya kamata, da amsa kiran jama’a, da kuma shawo kan matsalolin kyale moriyar jama’ar kasar. (Zainab)