logo

HAUSA

Budaddiyar Kasuwar Kasar Sin Za Ta Samar Da Damarmaki Ga Kamfanonin Kasashen Waje

2022-03-05 11:12:30 CRI

Rahoton aiki da gwamnatin kasar Sin ta mika ga majalisar dokokin kasar wato majalisar wakilan jama’ar kasar Sin domin nazari a yau Asabar, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta amfana sosai da jarin kasashen waje. Kuma za ta duba yuwuwar nazarin bangarorin da kasashen waje ba za su iya zuba jari ba, domin tabbatar da an ba su damarmaki kamar takwarorinsu na cikin gida.

A cewar rahoton, kasar Sin za ta inganta hadin gwiwa karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, da kara jajajircewa kan ka’idar samun ci gaba na bai daya ta hanyar tuntuba da hadin gwiwa.

Baya ga haka, kasar za ta zurfafa gyare-gyare domin saukaka hanyoyin biyan harajin kwastam da gina wani tsarin jigilar kayayyaki na kasa da kasa, domin rage kudin da ake kashewa da kara inganta cinikayya da kasashen ketare

Rahoton ya kara da cewa, yarjejeniyar tattalin arziki ta RCEP, ta samar da wani yankin ciniki mara shinge mafi girma a duniya. Kuma kasar Sin za ta karfafa gwiwar kamfanoni su yi amfani da fifikon haraji da na asalin kayayyaki, da sauran ka’idojin dake karkashin yarjejeniyar, domin fadada hadin gwiwa kan cinikayya da zuba jari.

Har ila yau, kasar Sin za ta tattauna tare da cimma yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci mai inganci da karin kasashe da yankuna.

Bugu da kari, rahoton ya ruwaito cewa, a shirye Sin take ta hada hannu da sauran kasashe wajen inganta hadin gwiwa da cimma sakamako na moriyar juna ga kowa. (Fa’iza Mustapha)