logo

HAUSA

Kakaki: Mutane su ne ke da ikon fada a ji a tsarin demokaradiyya

2022-03-04 16:01:13 CRI

 

Kakakin kasar Sin ya ce, ko kasa tana bin tsarin demokaradiyya ko ba ta bi, abubuwan da ake aiwatarwa ne za su tabbatar da hakan kuma mutanen wannan kasa su ne ke da ikon fada a ji.

Baki dayan tsarin demokaradiyyar kasar Sin ya ta’allaka ne bisa ga bin kyakkyawan tsari, tare da bai wa al’umma damar shiga a dama da su, a cewar Zhang Yesui, kakakin taro na 5 na zaman majlisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 13, wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai a yau Jumma’a a Beijing.

Zhang ya ce, demokaradiyya ba wani abin ado ba ne, demokaradiyya ya shafi batu ne na daidaita matsalolin al’umma.(Ahmad)