logo

HAUSA

Majalisar wakilan jama’ar kasar Sin za ta fara zama na tsawon kwanaki 6 da rabi

2022-03-04 13:59:10 CRI

Majalisar dokokin kasar Sin, za ta fara zamanta na shekara-shekara, daga safiyar gobe Asabar a birnin Beijing.

Kakakin majalisar na 13, Zhang Yesui, ya ce an tsara za a kammala zama na 5 na majlisar da ake kira majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC), a ranar 11 ga watan Maris, inda za a nazarci batutuwa 10.

A cewar Zhang Yesui, wakilan jama’a na majalisar za su nazarci daftarorin da suka hada da rahoton ayyukan gwamnati tare da tattaunawa kan yi wa dokar kula da harkokin kauyuka da na gwamnatocin kananan hukumomi gyaran fuska.

Za kuma su tattauna kan daftarin yanke shawara game da adadin wakilan jama’a na majalisar karo na 14 da batun zabensu, da kuma wasu daftarori biyu da suka shafi zaben wakilan jama’a na yankin musamman na HK da Macao a majalisar ta 14. (Fa’iza Mustapha)