Gasar Olympics Ta Nakasassu Ta Lokacin Hunturu Ta Beijing Ta Nuna Nasarar Da Sin Ta Cimma A Fannin Kare Hakkin Dan Adam
2022-03-04 13:50:14 CRI
A daren yau ne, za a bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin hunturu ta Beijing a hukumance, inda ’yan wasan motsa jiki daga kasashen duniya za su yi kokarin samun nasara a wannan dandali mai muhimmanci.
Shugaban kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na kasa da kasa Andrew Parsons ya ce, masu aikin sa kai na birnin Beijing suna da himma da kwazo, yadda suke gudanar da ayyukansu, ya nuna min yadda al’ummar Sin suke karbar baki da hannu bibbiyu.
Kasar Sin ta dukufa wajen shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu bisa ka’idojin kare muhalli, yin hadin gwiwa, bude kofa ga waje, da kuma yaki da cin hanci da karbar rashawa, ta yadda za a tallafawa ’yan wasannin motsa jiki na nakasassu kamar yadda suke bukata.
Haka kuma, za a ci gaba da amfani da na’urorin da aka yi amfani da su a gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu, da kuma gyara su domin dacewa da bukatun nakasassu.
Gwamnatin kasar Sin ta kuma fidda takardar bayani mai taken “wasannin masu bukatar musamman”, inda aka yi cikakken bayani kan yadda aka raya wasannin motsa jiki tsakanin rukunin mutane masu bukata ta musamman, da kuma taimaka musu cimma burikansu.
Ana sa ran cewa, gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin hunturu da za a yi a birnin Beijing, za ta kara kwarin gwiwa tsakanin rukunin mutane masu bukata ta musamman, da kara fahimtar da gamayyar kasa da kasa game da bukatun mutane masu bukata ta musamman. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)