logo

HAUSA

Daukar kasar Sin a matsayin abokiyar adawa zai lalata dangantaka da aminci tsakaninta da Amurka

2022-03-04 14:06:24 CRI

Kakakin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin a zamanta na 5, Zhang Yesui, ya ce daukar kasar Sin a matsayin abokiyar adawa, zai lalata aminci da dangantakar dake tsakaninta da Amurka, yayin da tsayayyar dangantaka a tsakaninsu, za ta dace da ci gaban kasashen biyu da samar da kyakkyawan yanayin tabbatar da zaman lafiya a duniya. 

Zhang Yesui ya bayyana haka ne a yau Juma’a, yayin wani taron manema labarai a nan Beijing. (Fa’iza Mustapha)