logo

HAUSA

An Gudanar Da Bikin Bude Gasar Wasannin Olympics Ta Lokacin Sanyi Ta Nakasassu Ta Shekarar 2022 Ta Beijing

2022-03-04 21:28:48 CRI

Da yammacin yau ne, aka yi bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta nakasassu ta Beijing na shekarar 2022 a filin wasa na kasa da kasa dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da bude gasar.

Bikin wanda Zhang Yimou ya jagoranta, yana da taken "Blossoming of Life" an kuma kasa shi zuwa gida 12. Daga cikin masu shirya bikin su 800, kashi 30 cikin 100 mutane ne masu nakasa, kuma an yi haka ne don nuna hadin kai a cikin al'umma.

Gasar wasannin Olympics ajin nakasassu na lokacin sanyi na Beijing, za ta gudana har zuwa ranar 13 ga Maris, tare da 'yan wasa na kasa da kasa da za su fafata a wasanni 78 a manyan wasanni har guda 6, wadanda suka hada da wasan zamiya, da wasan zamiya na yada kanin wani, biathlon, snow boarding, da wasan kwallon gora na kankara na nakasassu, da curling na keken guragu.(Ibrahim)