logo

HAUSA

Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta kaddamar da zamanta na shekara-shekara

2022-03-04 19:51:31 CRI

Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, ta fara zamanta na shekara-shekara, yau Juma’a a birnin Beijing.

 

Shugaba Xi Jinping da sauran shugabannin kasar Sin sun halarci taron bude zama na 5 na kwamitin kasa na majalisar ta 13, wanda ya gudana a babban dakin taron jama’ar kasar Sin.

 

Yayin taron kuma, shugaban kwamitin majalisa, Wang Yang, ya gabatar da rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalisar. 

 

Wang Yang ya ce, shekarar 2022 muhimmiyar shekara ce da Sin ta shiga lokacin zamanintar da kasa bisa tsarin gurguzu a dukkan fannoni da kuma kokarin cimma burin kafa kasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani mai wadata, bin tsarin demokuradiyya, wayin kai da jituwa nan da shekarar 2049 wato yayin da za a cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, kana jam’iyyar kwaminis ta Sin za ta gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar na dukkan kasar karo na 20. Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin tana bin jagorancin tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki, da kiyaye gudanar da ayyuka yadda ya kamata, da tsayawa tsayin daka kan hadin kai da tabbatar da demokuradiyya, da sa kaimi ga ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar don cimma daidaito, da gudanar da ayyukan bisa tunanin kasar, da hadin kan al’ummar kasar, da ba da shawara kan harkokin siyasa, da kuma samar da hidima kan fannoni daban daban.