logo

HAUSA

Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta kaddamar da zamanta na shekara-shekara

2022-03-04 15:50:30 CRI

 

Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, ta fara zamanta na shekara-shekara, yau Juma’a a birnin Beijing.

Shugaba Xi Jinping da sauran shugabannin kasar Sin sun halarci taron bude zama na 5 na kwamitin kasa na majalisar ta 13, wanda ya gudana a babban dakin taron jama’ar kasar Sin.

Yayin taron, an nazarci ajandar zaman majalisar, tare da amincewa da ita.

Yayin taron kuma, shugaban kwamitin majalisar na kasa, Wang Yang, ya gabatar da rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalisar.