logo

HAUSA

Xi ya tattauna harkokin kasa da mambobin CPPCC

2022-03-03 10:50:06 CRI

 

Gobe Juma’a 4 ga wata, za a kaddamar da taro karo na 5, na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 13 a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A cikin shekaru 9 da suka gabata, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya riga ya saba da yin tattaunawa kan harkokin kasa da mambobin majalisar, wadanda ke halartar taron.

Yayin taruka biyu na shekarar 2013, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping, ya shiga taron mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, da suka fito daga bangarorin kimiyya da fasaha, inda ya bayyana cewa, “Ya zama wajibi a nace kan manufar yin kirkire-kirkire mai salon kasar Sin, domin kara zurfafa kwaskwarima kan tsarin kimiyya da fasaha, ta yadda za a cimma burin raya kasar Sin, daga kasa da take mai da hankali kan tattalin arziki zuwa kasa mai ci gaban tattalin arziki.”

Ya zuwa shekarar 2014, Xi ya tattauna harkokin kasa da mambobin majalisar ‘yan kananan kabilu sama da 100, inda ya nuna kaluwa kan batun samun aikin yi na daliban ‘yan kananan kabilun yankin Xinjiang na kasar, ga tambayoyinsa: “Ko yawancin daliban da suka kammala karatu a jami’a sun koma yankin Xinjiang? Adadin su ya kai nawa a ko wace shekara?”

Xi ya jaddada cewa, dole ne a yi kokari matuka domin hanzartar ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar yankunan da ‘yan kananan kabilun kasar ke cunkoso.

Yanzu haka za a kaddamar da taruka biyu na bana, wadanne irin batutuwa Xi zai tattauna da mambobin? Kuma wadanne irin ra’ayoyi masu hikima zai gabatar? Bari mu jira mu gani. (Jamila)