logo

HAUSA

Sin ta ciri tuta wajen tallafawa masu bukata ta musamman

2022-03-03 18:46:17 CRI

Ga duk mai bibiyar manufofin kasar Sin, wadanda suka jibanci kara inganta rayuwar al’umma, ba zai gaza lura da yadda mahukuntan kasar ke bullo da shirye-shirye daki daki ba, na kyautata rayuwar sassan al’ummun ta masu bukatu na musamman, da suka hada da masu nakasar sassan jiki, ko rashin lafiya, ko tsufa.

Akwai tarin manufofi da mahukuntan kasar ke tsarawa, domin ganin dukkanin sassan masu bukatar musamman a kasar sun more rayuwa mai inganci cike da walwala.

Ga misali, kasar Sin ta tsara shirye shirye na musamman, domin kula da lafiyar tsofaffi, musamman wajen samar musu da hidimomin rayuwar yau da kullum, da matsugunai masu inganci, da kula da lafiya, da inganta unguwannin da suke zaune, da samar da inshorar lafiya da dai sauran su.

A bangaren wasanni, a ranar Alhamis din nan, majalissar gudanarwar kasar Sin ta fitar da takardar bayani mai kunshe da fashin baki, game da irin ci gaban da kasar ta samu, a bangaren raya sha’anin wasanni, tsakanin rukunin mutane masu bukata ta musamman.

Takardar na zuwa a gabar da ake daf da bude gasar Olympics ta shekarar 2022, ajin masu bukatar musamman ko Paralympic, wadda birnin Beijing ke karbar bakunci.

Ko shakka babu, tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, an rika samun manyan nasarori a fannonin kyautata rayuwar masu bukata ta musamman, inda gwamnatin kasar Sin ke kara bunkasa harkokin wasannin wannan rukuni na al’ummar Sinawa, bisa halin da kasar ke ciki da ma bukatu na zamantar da rayuwa.

Irin wadannan manufofi da tsare-tsare, da gwamnatin Sin ke aiwatarwa, nasarori ne manya da suka zamo “zakaran gwajin dafi” a tarihin duniya, wato batun tafiya tare da dukkanin sassa, da rukunonin al’ummar kasa ba tare da nuna wariya ba, kamar dai yadda sau da dama, a kan ji shugaban kasar Sin Xi Jinping na nanata cewa, burin gwamnatin kasar Sin shi ne inganta rayuwar al’ummar ta, ba tare da barin kowa a baya ba! (Saminu Hassan)