logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya amince da kashe dala miliyan 8.5 domin kwashe ‘yan kasar daga Ukraine

2022-03-03 15:12:34 CRI

 Rahoton jaridar “Vanguard” ta tarayyar Najeriya, ya bayyana cewa, jiya Laraba mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo, ya kira taron kwamitin zartaswa na tarayyar Najeriya ta kafar bidiyo a fadar shugaban kasar, daga baya karamin ministan harkokin wajen kasar Zubairu Dada, ya fayyacewa manema labarai cewa, shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya riga ya amince da kashe kudi har dalar Amurka miliyan 8.5, domin kwaso ‘yan kasar sama da su 5000 dake zaune a Ukraine zuwa gida, inda ya bayyana cewa, yanzu haka kamfanin Air Peace na Najeriya, da kamfanin Max, sun riga sun daddale kwangilar yin jigilar, an kuma alkawarta cewa, za a samar da jiragen sama guda uku, domin gudanar da aikin. (Jamila)