logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira da a warware batun Ukraine ta hanyar yin shawarwari

2022-03-03 11:00:35 CRI

Jiya Laraba, an kada kuri’u kan daftarin batun Ukraine, yayin taron gaggawa na musamman karo na 11, wanda babban taron MDD ya kira. Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya halarci taron, inda ya janye jiki daga kada kuir’a, da kuma bayyana ra’ayin kasar Sin kan wannan batu.

Ya ce, ya kamata MDD da bangarorin da abun ya shafa, su dauki matakai bisa ka’idar kare zaman lafiya, da zaman karko na yankin, amma, cikin wannan daftarin da aka fidda, ba a fahimci sabanin dake tsakanin bangarorin da abun ya shafa yadda ya kamata ba, kuma ba a mai da hankali wajen gaggauta aikin warware matsalar ta hanyar siyasa, da karfafa matakan diflomasiya ba.

Ya kuma jaddada cewa, ya kamata a yi watsi da tunanin yakin cacar baka, domin warware matsalar Ukraine daga tushe, kuma matsa wa bangarorin da abun ya shafa lamba, da kuma neman raba tsakaninsu, za su kara fadada sabanin dake tsakaninsu, da haifar da illa ga karin kasashen duniya. (Maryam)