logo

HAUSA

Sin ta fitar da takardar bayani game da wasannin masu bukatar musamman

2022-03-03 11:22:55 CRI

A Alhamis din nan ne kasar Sin ta fitar da takardar bayani mai taken wasannin masu bukatar musamman, wadda ke kunshe da fashin baki game da irin ci gaban da kasar ta samu, a bangaren raya wasanni tsakanin rukumin mutane masu bukata ta musamman.

Majalissar gudanarwar kasar Sin ce ta fitar da takardar bayanin, kwana guda kafin bude gasar Olympics ta 2022, ajin masu bukatar musamman ko Paralympic, wadda birnin Beijing ke karbar bakunci.

Takardar bayanin ta ce, tun bayan kafuwar jamhuriyar jamaar kasar Sin a shekarar 1949, ake ta samun ci gaba a fannonin kyautata rayuwar masu bukata ta musamman, kuma kasar Sin ke kara bunkasa wasannin wannan rukuni na alummarta, bisa halayyar musamman ta kasar, da kuma martaba tafiya da zamani.

Kaza lika takardar bayanin ta tabo irin nasarori da aka cimma a tarihi, a bangaren raya wasannin masu bukatar musamman tun bayan taro na 18, na JKS da ya gudana a shekarar 2012.    (Saminu)