logo

HAUSA

Sau 11 da aka gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta nakasassu a Sin

2022-03-03 15:25:32 CRI

Cikin takardar da ofishin yada labarai na gwamnatin kasar Sin ya fitar a yau Alhamis, an ce kasar Sin ta ba da muhimmiyar gudummawa ga bunkasar harkokin motsa jiki na nakasassu a fadin duniya. Daga shekarar 2016 zuwa shekarar 2020, tawagar ’yan wasan motsa jiki ta nakasassu ta kasar Sin, ta halarci gasannin kasashen duniya guda 160, inda suka lashe lambobin yabo na zinari guda 1,114. Kuma, tun daga shekarar 1984 da aka fara gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta nakasassu a kasar Sin, ya zuwa yanzu, gaba daya an gudanar da gasanni sau 11 a cikin kasar.

Haka kuma, kakakin kungiyar hadin gwiwar nakasassu ta kasar Sin Guo Liqun ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da matukar hankali wajen kare ikon nakasassu, da samar da wani yanayi na kawar da duk matsaloli ga nakasassu, da kuma ba da tallafi gare su. (Maryam)