logo

HAUSA

Jami’an tsaron Najeriya sun hallaka sama da ’yan bindiga 200 a jihar Neja

2022-03-03 10:30:46 CRI

Kwamishinan kananan hukumomi na gwamnatin jihar Neja dake shiyyar tsakiyar Najeriya Emmanuel Umar, ya ce jamian tsaron kasar sun yi nasarar hallaka sama da yan bindiga 200, yayin wani simame na hadin gwiwa da suka gudanar a jihar tsakanin ranekun Lahadi zuwa Talata.

Mr. Umar, wanda ya bayyana hakan ga yan jaridu a jiya Laraba a birnin Minna, fadar mulkin jihar ta Neja, ya ce jamian tsaro 2 sun rasu yayin artabun, kana wasu kalilan sun samu raunuka daban daban.

Kwamishinan ya kara da cewa, akwai karin wasu yan bindigar da dama da suka tsere da harbin bindiga a jikin su, don haka ya bukaci alumma da su kai rahoton duk wata bakuwar fuska da ba su amince da ita ba ga jamian tsaro, duba da cewa, yakin da ake yi da bata gari ba na gwamnati ne kadai ba.    (Saminu)