logo

HAUSA

Kasar Sin Na Fatan Wadanda Suka Kitsa Za Su Yi Tunani Game Da Rawar Da Suka Taka A Rikicin Ukraine

2022-03-03 20:51:26 CRI

Dangane da yadda kafafen yada labarai na yammacin duniya ke yiwa fahimtar bangaren Sin game da shirin daukar matakin soja na kasar Rasha bahaguwar fahimta, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin, ya jaddada a yayin taron manema labaru da aka saba yi Alhamis din nan cewa, yana fatan wadanda suka haddasa rikicin, za su yi tunani kan rawar da suke takawa a cikin rikicin kasar ta Ukraine, su dauki nauyin rikicin a zahiri, su kuma yi aiki tare da daukar matakai na zahiri don sassauta lamarin da magance matsalar, maimakon zargin wasu.

Haka kuma, Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta damu da yadda "Amurka za ta kori jami'an diflomasiyya 12 daga tawagar dindindin ta Rasha a MDD. A matsayinta na wadda MDD ke cikin kasarta, ya kamata Amurka ta aiwatar da yerjejeniyar da aka cimma tsakanin MDD da Amurka kan hedkwatar ta MDD da gaskiya, ta samar da kyakkyawan yanayi da kuma tabbacin gudanar da ayyuka na yau da kullum ga jami'an diflomasiyya na kasashe mambobi, a maimakon yin amfani da ikonta wajen yanke hukunci na kashin kai a matsayin kasa mai masaukin baki. (Ibrahim)