logo

HAUSA

Farfadowar Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Taimakawa Wajen Daidaita Ayyukan Yi

2022-03-03 20:40:47 CRI

Kakakin taro zama na biyar na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin (CPPCC) karo na 13 Guo Weimin ya bayyana cewa, yadda kasar Sin ke ci gaba da farfado da tattalin arzikinta, da samun bunkasuwa mai karfi a sabbin masana'antu, da tsarin kasuwanci, zai taimaka wajen daidaita ayyukan yi, ta hanyar samar da karin guraben ayyukan yi.

Guo Weimin wanda ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, ya kuma bayyana cewa, kasar Sin tana ba da fifiko matuka kan batun samar da aikin yi, haka kuma ta fitar da manufofi da matakai yadda ya kamata.

Mambobin CPPCC sun ba da shawarar cewa, a ba da kulawa ta musamman ga muhimman rukunoni, kamar daliban da suka kammala jami'a, da ma'aikata bakin haure da masu fama da matsaloli, inda suka yi kira da a taimaka wa rukunin wadannan mutane. (Ibrahim)