logo

HAUSA

Tawagar Rasha ta isa Belovezhskaya Pushcha don shiga zagaye na 2 na tattaunawa kan batun Ukraine

2022-03-03 10:22:15 CRI

Mataimaki ga shugaban kasar Rasha, kuma jagoran tawagar kasar a tattaunawa da tsagin Ukraine Vladimir Medinsky, ya ce tawagar da yake shugabanta ta isa Belovezhskaya Pushcha, dake kan iyakar Belarus da Poland, domin shiga tattaunawa karo na biyu da wakilan Ukraine.

Mr. Medinsky ya ce, Rasha da Ukraine sun amince da wurin da za a hadu domin gudanar da shawarwarin, yayin da sojojin Rasha ke samar da dama ga wakilan Ukraine, ta halartar su wurin da aka tsara ganawar.

Medinsky ya kara da cewa, akwai tsammanin za a tattauna game da yiwuwar tsagaita bude wuta yayin zaman na biyu, tare da sauran muhimman batutuwa.   (Saminu Fagam)